• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAIGARI: GASKIYA WASU ‘YAN SARS SUN WUCE GONA DA IRI

Ministan ‘yan sandan Najeriya Muhammadu Maigari Dingyadi ya ce hakika wasu daga ‘yan SARS sun wuce gona da iri a lokacin gudanar da aikin su.

Dingyadi da ke magana da ‘yan jaridar kafafen turai, ya ce wannan dalili zarmewar ta ‘yan SARS ya sanya rushe rundunar. Ministan wanda bai faye magana ba sai kwanan nan, ya ce za a binciko wadanda su ka ingiza aikata zanga-zangar da ta kai ga cutar da jama’a don fuskantar hukunci.

Maigari Dingyadi da ya taba tsayawa takarar gwamnan Sokoto a inuwar jam’iyyar DPP ta Alhaji Attahiru Bafarawa, ya ce ‘yan sandan Najeriya na da kwarewar aiki amma a kan samu wake daya ne mai bata miya.

Dingyadi ya kara nanata cewa lalle jami’an sabuwar rundunar SWAT da ta maye gurbin SARS za ta zama da nagartattun jami’ai ne kuma duk wanda ya taba yin SARS ba zai samu shiga sabuwar rundunar ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “MAIGARI: GASKIYA WASU ‘YAN SARS SUN WUCE GONA DA IRI”
 1. Hello very nice site!! Guy .. Excellent .. Amazing .. I’ll bookmark your blog and take the feeds additionally?
  I’m happy to find numerous helpful info here within the submit, we want
  develop extra strategies on this regard, thanks for sharing.
  . . . . .

 2. I’m not sure why but this blog is loading incredibly slow for me.
  Is anyone else having this problem or is it a problem on my end?
  I’ll check back later on and see if the problem still exists.

 3. Pretty nice post. I just stumbled upon your weblog and wished to say that I have
  really enjoyed browsing your blog posts. After all I’ll be subscribing to your rss feed
  and I hope you write again very soon!

Leave a Reply

Your email address will not be published.