Farfesa Mahmud Yakubu ya kama hanyar samun wa’adi na biyu a matsayin shugaban hukumar zaben Najeriya INEC.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tura sunan Farfesa Yakubu ga shugaban majalisar datttawa don tantance shi ya cigaba da shugabancin hukumar zaben a sabon wa’adi.
Farfesa Yakubu ya hau kujerar bayan zaben 2015 inda ya maye gurbin Farfesa Attahiru Jega wanda ya kammala wa’adi ya bar hukumar a hannun riko.
Wannan ya nuna Farfesa Yakubu ne a ke sa ran zai gudanar da babban zaben Najeriya a 2023 bayan na 2019 da ya gudanar, kamar yanda Attahiru Jega ya samu gudanar da na 2011 da 2015.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
This actually answered my downside, thank you!