• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAHAMAT DERBY YA GANA DA SHUGABA BUHARI

Shugaban mulkin soja na Chadi Mahamat Derby ya gana da shugaban Najeriya a fadar Aso Rock karo na farko tun kashe mahaifin sa Idris Derby.

Shugaba Buhari bai kushe mulkin soja na Chadi kai tsaye ba, amma ya bukaci a bi tsari cikin ruwan sanyi na maida mulki hannun farar hula.

Da alamun kasashe na takatsantsan kan lamarin kushe mulkin soja a Chadi in an duba yanda a ka yi wa Derby kisan gilla.

Faransa da ta yi wa Chadi mulkin mallaka na mara baya ga mulkin sojan don samun tsayawar madafun iko da gudun aukawa babbar fitina.

Tun farko Mahamat Derby ya gana da shugaban Nijar Bazoum Muhammad a birni Yamai.

Mahamat Derby na rangadin makwabta na tafkin Chadi don zanta lamuran hadin kai da tsaron yankin daga hare-haren ‘yan ta’adda.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.