• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAHAIFIYA TA NA DA JININ KANURI- SHUGABA MUHAMMADU BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tuna baya inda ya tabo tarihin sa da baiyana alakar mahaifiyar sa da barebari.

Shugaban wanda ke magana a fadar Shehun Borno Alhaji Garbai Umar Elkenemi, ya ce mahaifiyar sa ta hada jinin barebari da na hausawa don haka ya ke da dangantaka da Borno.

Shugaba Buhari ya ce amma ta bangaren mahaifin sa mallam Adamu Bafulatani ne 100% da hakan ya ba shi damar iya zolayar dukkan kabilun.

Hakanan shugaban ya tuno lokacin da ya zama gwamnan soja a yankin a zamanin marigayi Janar Murtala Muhammed.

Shugaban ya ce ya sha kwaramniyar duniya har lokacin da ya tsaya takarar zabe da zuwan sa kara kotun koli har sau uku.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *