• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MAGAJIN TSOHON MINISTA SALE MAMMAN WATO INJINIYA MU’AZU JAJI YA ZO

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zabo Injiniya Mu’azu Jaji Sambo a matsayin sabon minister daga jihar Taraba don maye gurbin tsohon ministan lantarki Saleh Mamman da ya sauke daga mukamin tare da tsohon ministan gona Sabo Nanono.
Shugaban ya tura sunan Mu’azu Jaji Sambo gaban majalisar dattawa, inda tuni shugaban majalisar Ahmed Lawan ya gabatar da sunan don amincewa.
Za a jira ma’aikatar da za a tura sabon ministan mai daraja ta daya.
A baya dai shugaba Buhari kan dau dogon lokaci kafin maye gurbin minister in an tuna abun da ya faru bayan tafiyar tsohuwar minister muhalli Amina Muhammed majalisar dinkin duniya, da kuma hatsarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar karamin ministan kwadago daga jihar Kogi Barista James Ocholi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *