• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MACE TA ZAMA ‘YAR TAKARAR JAM’IYYAR APC A JIHAR ADAMAWA

Mace ta zama ‘yar takarar jam’iyyar APC a jihar Adamawa bayan gudanar da zaben fidda gwani da wakilin jam’iyya Gambo Lawal ya jagorantar.

Sanata Aisha Ahmad Binani ta lashe kuri’u masu rinjaye a zaben inda ta yi zarra kan tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu, tsohon gwamnan jihar Bindow Jibrilla da dan majalisar wakilai Abdulrazak Namdas.

Binani wanda a yanzu haka ‘yar majalisar dattawa ce daga jihar, ta bukaci sauran ‘yan takara su mara ma ta baya don APC ta lashe zabe.

Wannan ba shi ne karo na farko da mace kan samu tikitin takara a arewa maso gabar ba don marigayiya Aisha Jummai Alhassan ta taba samun tikitin a jihar Taraba a 2015.

Hakan ya nuna Binani za ta kara da gwamnan jihar Umar Fintiri na babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.