• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MACE MAI FARAR KAFA, GASKIYA NE KO CAMFI NE?

Byadmin

Jul 24, 2021 , , , ,

Babban limamin masallacin jumma’a a Bolari Gombe Sheikh Abubakar Lamido ya ce sam ba wani abu wai shi mata mai farar kafa kawai lamarin camfi ne da ya sabawa Islama.

A hudubar sallar jumma’a, Sheikh Lamido ya ce sam babban kuskure ne magidanci ya dorawa matar sa kagen cewa ta na da farar kafa shi ya sa matsalolin fatara ke damun sa.

Shehun malamin ya kara da cewa Allah mahaliccin dukkkan talikai ke da ikon kan komai don haka dogara ga Allah shi ne mafita kadai.

Malamin ya ce za ka ga an gwada cewa mace za ta haifi namiji sai ta haifi mace ko a ce za ta haifi mace sai ta haifi namiji, da hakan ke nuna Allah ke bayarwa kuma shi ke hukunta lamura bisa kudurar sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *