Ma’aikatar ilimin Najeriya ta amince da kafa cibiyar koyon lamuran aikin aiki karkashin kulawar hukumar alhazan ta Najeriya NAHCON.
Cibiyar za ta zama dama ga jama’a wajen samun limin gudanar da aikin hajji da ke daya daga rukunan musulunci 5.
An gudanar da taron karbar wannan bayani na amince a dakin taron hukumar alhazan da ke babban ofishin ta a Abuja mai suna ‘HAJJ HOUSE’
Shugaban hukumar alhazan Zikrullah Kunle Hassan, jagoran cibiyar Dr.Aliyu Tanko da sauran jami’an hukumar alhazan sun shaida taron.
An kirkiro tsarin kafa cibiyar koyar da ilimin aikin hajji zamanin tsohon shugaban hukumar Abdullahi Muktar Muhammad.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀