Bisa umurnin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da musamman kungiyar ma’aikatan lantarki, ma’aikatan lantaki na jihar Kaduna sun auka yajin aiki.
Yajin aikin na gargadi don nuna rashin amincewa ne da muradin gwamnan Kaduna Nasir Elrufai na rage yawan ma’aikata.
Gwamna Elrufai ya ce ma’aikata na lashe makudan kudi daga kason jihar don haka za a samu rarar kudi in an rage yawan ma’aikata.
Ma’aikatan wutan na son jefa jihar Kaduna cikin duhu don jawo hankalin gwamnati ta janye abun da ta yi niyya.
Ma’aikatan filin jirgin saman Kaduna na son taya sauran ma’aikata gwagwarmaya inda su ma za su shiga yajin aiki.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀