• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MA’AIKATAN HUKUMAR KASUWANCIN TEKU SUN ZUBAR DA HAWAYE DA KAMMALA AIKIN HASSAN BELLO

Ma’aikatan hukumar kasuwancin teku ta Najeriya sun xubar da hawaye yayin da shugaban hukumar da ya kammala wa’adin aiki Mallam Hassan Bello ya ke bankwana da su.

Bello wanda ya shiga ofishin hukumar a Wuse Zone 5 Abuja don alamta kammala aiki lafiya, ya samu ma’aikata na juyayin rabuwa da shi don yanda ya yi aiki da su tsawon shekaru da kirkiro shirye-shirye da su ka sa kowa ya zama cikin hidima a duk ranakun aiki.

Ma’aikatan sun yi wa Bello fatan alheri a aiyukan da zai gudanar a gaba yayin da ya shiga mota ya kama hanyar ficewa da helkwatar.

Rahoto ya baiyana cewa Bello ya kaucewa zuwa ofishin hukumar a Lagos don kar juyayin ya kara yawa har shi din ma ya zubar da hawayen.

Cikin aiyukan da ya kirkiro akwai tabbatar da kafuwar tashoshin sauke hajar teku a yankunan arewacin Najeriya da ba sa bakin teku, kafa tashoshin hutawar manyan motoci don rage hatsari a kan manyan tituna, yaki don a rage harajin fiton kaya, tallafawa wajen tura kayan Najeriya ketare don sayarwa da yunkurin kafa hukuamr sufuri da sauran su.

Bello ya sha nanata cewa matukar za a bunkasa sasahen sufuri, to zai iya kawowa Najeriya riba fiye da man fetur.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
56 thoughts on “MA’AIKATAN HUKUMAR KASUWANCIN TEKU SUN ZUBAR DA HAWAYE DA KAMMALA AIKIN HASSAN BELLO”

Leave a Reply

Your email address will not be published.