• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MA’ABOTA MOTOCI DA BABURA SUN KOKA KAN SHAN MAN FETUR MARAR KYAU

Ma’abota motoci da babura a sassan Najeriya na kokawa kan yiwuwar shan man fetur marar kyau da hakan ya haddasa matsala ga injinan su.
Wannan labari ma ya biyo bayan wani labarin da ke nuna an samu wani man fetur da ya jirkita da ruwa da ya sa motoci tsayawa cak a babban birnin Najeriya Abuja.
Wani mai mota a Sokoto Anas Dan Nayaba ya baiyana shan irin wannan man da ya ce ya rikita ma sa injin motar sa fijo inda ya dau hoton man da ya sauya kala zuwa mai duhu.
Labarin masu korafi na nuna akalla man kan lalata kaifin na’urar tura mai da ya kan sa mota mutuwa a kan titi ko ta rika jijjiga.
Jami’in kungiyar dillalan mai ta Najeriya IPMAN Alhaji Bashir Salisu ya ce sun sami labarin amma bayan sun kammala bincike za su baiyana hakikanin abun da ya faru.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MA’ABOTA MOTOCI DA BABURA SUN KOKA KAN SHAN MAN FETUR MARAR KYAU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.