• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

LOKACIN AMAI DA GUDAWA DA ZAZZABI MAI ZAFI YA ZO

Yayin da a ke samun ruwan damuna ya na gangara zuwa wajajen da mutane ke amfani da ruwan sha.

Lamarin na faruwa ne domin ruwan da ke malala na daukar kwayoyin cuta ya shigar da su cikin ruwan da in mutane su ka sha za su samu cutar.

Cutukan sun hada da barkewar amai da gudawa da kuma zazzabi mai zafi wato “Tyhoid” wanda tsananin sa kan iya huda hanjin mutum.

Ya na da muhimmanci mutane su rika kare ruwan da su ke sha daga wani datti da ke dauke da kwayoyin cutuka.

Jami’an lafiya na ba da shawarar hanyoyin tsabtace ruwan sha da su ja hada da tace ruwan ta hanyar kyalle mai tsabta, tafasa ruwan ya yi sanyi a sha ko ajiye ruwan ya kwanta sai a debi na sama a yi amfani da shi don za a iya samun wasu kwayoyin cuta su koma can kasa su kwanta.

Kazalika ya na da kyau a tabbatar an tona rijiya mita 100 daga shadda ko salga hakanan in dabba mai cuta ta mutu a tona rami mai zurfi a bunne ta.

Yanzu haka an ba da labarin bullar amai da gudawa a Kano.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.