• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

LITAR FETUR ZA TA KAI NAIRA 320-340 A 2022-MELE KYARI KOLO

ByNoblen

Nov 24, 2021

Karshe dai shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPC Mele Kyari Kolo ya ce litar man fetur za ta kai Naira 320-340 a badi shekara ta 2022.
An dade a na hasashen tashin farashin litar fetur da kan sa NNPC fitowa wata-wata ta na cewa babu dai niyyar karin a lokacin.
Kyari ya ce zuwa karshen watan Febreru na badi biyan kudin tallafin fetur zai zama ba ya tsarin dokokin Najeriya.
Wannan na nuna gwamnatin za ta janye dukkan tallafin da hakan zai cilla litar ta kai Naira 340.
Hakika irin wannan yanayi kan haddasa mafi munin tashin farashin muhimman kayan masarufi da jefa talakawa da su ka yawa a kasar cikin kunci.

 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *