• Thu. Sep 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

LIMAMAI SUN YI KIRA GA BIN TSARIN SHUGABANCI A LAMURAN GANIN WATAN RAMADANA DA SHAWWAL

Limamai a masallatai idi daban-daban sun yi kira ga dukkan musulmi su rika bin tsarin shugabanci wajen daukar azumi ramadan da ajiyewa a ganin watan shawwal don kaucewa haddasa rudani.
Kiran ya biyo bayan yanda wasu kalilan a malamai sun yi umurni ga mabiyan su, su ajiye azumi a ranar lahadi sabanin umurnin jagoran musulmi wato Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar.
Malaman sun ce bisa ka’idar shari’a shugaban musulmi ne ke da hakkin ba da sanarwar da za a yi amfani da ita ga dauka ko ajiye azumi.
Shugaban majalisar malamai na JIBWIS Dr.Jalo Jalingo ya fitar da sanarwa ta musamman kan muhimmancin bin jagoran musulmi kan wadannan lamuran na addini.
Shi ma na’ibin limamin masallacin APO Zone E Imam Abdullahi ya ce bin umurnin sarkin musulmi Sultan Muhammad Abubakar shi ne kawai mafita kuma da ya dace da koyarwa islama.
Imam Abdullah ya bukaci sanya bakin dukkan sassa a lamuran ganin wata don kawo maslaha da za ta kawo karshen rabuwar kawuna.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “LIMAMAI SUN YI KIRA GA BIN TSARIN SHUGABANCI A LAMURAN GANIN WATAN RAMADANA DA SHAWWAL”
  1. I intended to put you this tiny word to be able to thank you so much again for your personal extraordinary tactics you’ve contributed in this case. It has been certainly shockingly generous with people like you to grant easily precisely what a lot of people could have marketed for an e-book to help make some cash on their own, mostly considering the fact that you could have done it if you ever considered necessary. These things in addition served to become a easy way to be aware that other people online have a similar passion much like my personal own to know way more in terms of this matter. I think there are many more enjoyable periods up front for those who see your website.

Leave a Reply

Your email address will not be published.