Lebanon ta nada Najib Mikati a matsayin firaminista mai jiran gado bayan samun amincewar manyan masu ruwa da tsaki.
Mikati wanda ya taba zama firaminista har sau biyu, ya samu goyon bayan majalisar dokokin kasar da shugaban kasar Michel Aoun ya jagoranta.
Mikati na da gagarumin aikin farfado da kasar daga tabarbarewar tattalin arziki mai munin gaske a tarihi.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀