• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

LEBANON-A NA SA RAN FIRAMINISTA MIKATI ZAI KAFA GWAMNATI NAN GABA KADAN

ByNoblen

Jul 29, 2021

A na sa ran sabon firaministan Lebanon Najib Mikati zai kafa sabuwar gwamnati nan ba da dadewa ba don tsamo kasar daga kuncin tattalin arziki da dambarwar siyasa.

Mikati ya ce ya na shirin kafa gwamnatin bayan samun amincewar yawancin wadanda ya mika sunayen su a majalisar ministoci daga shugaban kasar Michel Aoun.

Najib Mikati wanda bai fito daga babban gidan siyasa ba duk da ya taba zama firaminista har sau biyu, ya ce da yardar Allah zai kafa gwamnati.

Sabon firaministan ya zo ne bayan murabus ko ajiye aikin da mutum biyu su ka yi daga ‘yan Ahlusunnah masu hakkin mukamin.

Farko Hassan Diab ya sauka bayan fashewar makamai a tashar ruwa ta Beirut inda fiye da mutum 200 su ka mutu. Sai kuma Sa’ad Hariri wanda ya jingine aikin kafa gwamnati bayan kasa jituwa kan majalisar ministoci da shugaba Aoun.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2,204 thoughts on “LEBANON-A NA SA RAN FIRAMINISTA MIKATI ZAI KAFA GWAMNATI NAN GABA KADAN”