• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

LAUYA YA BUKACI KOTU TA DAKATAR DA BABBAN SUFETON ‘YAN SANDAN NAJERIYA DAGA OFIS

Wani lauya mai suna Maxwell Okpara ya shigar da kara babbar kotun taraiya a Abuja ya na bukatar kotun ta dakatar da babban sufeton ‘yan sanda Muhammad Adamu daga shiga ofis don ya kammala shekarun ritaya.

A ranar daya ga watan nan Adamu ya cika shekaru 35 na ka’idar aiki da yin ritaya a tsarin Najeriya.

Maxwell ya bukaci kotun ta matsawa shugaba Buhari lamba ya nada sabon babban sufeto.

Kazalika kotun ta tilasta babban sufeton ya daina amsa sunan mukamin don tuni ya zama tsohon jami’in ‘yan sanda.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.