• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

LAURETTA ONOCHIE TA BAIYANA GABAN KWAMITIN MAJALISAR DATTAWA DON ZAMA KWAMISHINAR ZABE

Karshe dai  jami’ar labarun yanar gizo ta shugaba Buhari, Lauretta Onochie ta baiyana gaban kwamitin zabe na majalisar dattawa don tantancewa ta zama kwamishiniya a hukumar zabe.

Tun watan Oktobar bara, shugaba Buhari ya tura sunan ta gaban majalisar don a tantance ta ta samu wannan mukami mai muhimmanci.

Hakan ya jawo suka mai tsanani daga wasu kungiyoyi da babbar jam’iyyar adawa ta PDP da ke cewa nada ta ya dabawa doka don kasancewar ta ‘yar jam’iyyar APC da nuna fargabar ba za ta yi wa sauran jam’iyyu adalci ba.

Lauretta ta ce ita yanzu ba ta cikin harkar siyasa kuma ta sama mace mai bin ka’idar aiki sau da kafa.

Za a jira tabbatar tantance Lauretta daga kwamitin zaben karkashin Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “LAURETTA ONOCHIE TA BAIYANA GABAN KWAMITIN MAJALISAR DATTAWA DON ZAMA KWAMISHINAR ZABE”

Leave a Reply

Your email address will not be published.