• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

LAGOS NA KARA DAUKAR MATAKAN KAWO KARSHEN ZANGA-ZANGAR ENDSARS

Jihar Lagos da ta zama cibiyar zanga-zangar kauda SARS na kara daukar matakan kawo karshen zanga-zangar da ta rikita jihar da ke bakin tekun atalantika.

Yanzu haka dai gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya ba da umurnin dakatar da lamuran gwamnati in ban da lamuran tsaro.

Wannan ma ya biyo bayan kashe-kashe da a ka samu da a ka yi wa ‘yan zanga-zangar da hakan ya samu martani daga Amurka da majalisar dinkin duniya na bin kadun masu zanga-zangar.

Duk da dokar hana yawo, bai hana bullar masu zanga-zangar a wasu sassan birnin mai yawan jama’a ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.