• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

LAFIYA: MUTANE NA YAWAN KUKAN KAMUWA DA ZAZZABIN CIZON SAURO A NAJERIYA

ByNoblen

Sep 28, 2020

Akalla a kullum mutane kan shiga dakunan shan magani a yankunan Najeriya su nuna baiyana kukan fama da zazzabi wanda yawanci in an gwada ko yin tambayoyi sai a gano zazzabin cizon sauro ne.
Zazzabin dai ya fi yawaita ne a lokacin damuna don yanda ruwa kan kwanta da kan sanya hayaiyafar sauro.

Akwai kimanin mutum miliyan 100 da ke fama da cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya inda mutum dubu 300 kan riga mu gidan gaskiya duk shekara.

Zazzabin na sanadiyyar mutuwar kashi 11% na mata masu juna biyu da hakan kan ma yi saurin shafar jarirai. Wannan zazzabi ne mai zafi da kan kawo ciwon kai, hajijiya da kuma jin dari da kan sa mai fama son zama a rana.

Amfani da gidan sauro, maganin kashe sauro da tsabtace muhalli na taimakawa wajen rigakafin kamuwa da zazzabin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.