• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KWAMISHINIYAR MATA A ZAMFARA TA SAMU MUKAMIN KWAMISHINA A JIHAR TA TA ASALI IMO

Kwamishinyar mata da yara ta jihar Zamfara Hajiya Rabi Ibrahim Shinkafi ta sake samun mukamin kwamishinya a jihar ta, ta asali wato Imo.
Gwamnan jihar Imo Sanata Hope Uzodinma ne ya nada Rabi a wannan mukami cikin jerin sabbin kwamishinonin da ya nada.
Shinkafi ta ajiye mukamin ta na kwamishinya a jihar Zamfara da godewa damar da gwamna Matawallen Maradun ya ba ta, inda ta karbi mukamin da jihar ta, ta haihuwa ta ba ta.
Bayanai sun nuna Rabi Shinkafi ta zo jihar Zamfara ne sanadiyyar auren dan jihar inda har ta samu daukakar wannan mukami.
Shinkafi wacce ‘yan kabilar Igbo ne ta sauya suna zuwa na ‘yan arewa yayin da ta yi auren inda ta shiga addinin Islama.
Rabi ta yi watsi da cewa murabus ta yi amma maimakon haka ta karbi mukamin kwamishinya a Imo don haka ya zama ta ajiye mukamin jihar Zamfara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *