Hatsarin karamin jirgin ruwa a jihar Kebbi ya rutsa da fasinjoji 160 da akasari mata ne da kananan yara.
Matafiyan sun taso ne daga jihar Neja don zuwa yankin karamar hukumar Ngaski da ke jihar Kebbi.
A na fargabar mutane da yawa sun rasa ran su yayin da a ka samu nasarar ceto wasu daga cikin su.
Sau da dama irin wannan hatsari ya kan faru ne a sanadiyyar shake jirgi da fasinjojin da su ka wuce kima.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀