• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KUSHE BA DA KYAUTAR MOTOCI DA GWAMNA FINTIRI YA YI, YA JA RASA SARAUTAR MUKADDAS NA ADAMAWA

ByNoblen

Dec 13, 2021 ,

Matakin kushe kyautar motoci da gwamnan Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya rabawa sarakuna, ya ja wa Mukaddas na Adamawa Umar Mustapha rasa sarautar sa.
Gwamna Fintiri ya raba motocin shiga da na rakiya ga kowane daga sarakuna masu daraja ta daya a jihar.
Lamidon Adamawa Barkindo Aliyu Mustapha ya sauke mukaddas din don matakin kushewar ta sa ba amfanin ya cigaba da zama mai mukamin gargajiya.
Umar Mustapha dai ya nemi tikitin takarar gwamnan Adamawa karkashin jam’iyyar APC.
Mustapha a bayanin na sa ya ce ba daidai ne gwamnan ya kashe Naira miliyan 200 wajen sayan motoci ga sarakuna ba, alhali ‘yan fansho na mutuwa da yunwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.