• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KUSAN KULLUM SAI MUN SAMU ‘YAN NAJERIYA DA A KE DAWO DA SU DAGA KETARE – KONTUROLA

Konturolan hukumar shige da fice da ke kula da babban filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Lagos AM Usman ya ce kusan kullum sai an dawo da ‘yan Najeriya daga wasu kasashe don saba ka’ida.

Usman da ke zagayawa da manema labaru don duba yanda jami’an shige da fice ke gudanar da aiki a filin jirgin mai hada-hada dare da rana, ya ce jami’an sa kan zaunar da wadanda a kan dawo da su don ba su shawarwarin yanda za su rika kaucewa sabawa dokokin kasashen ketare da kuma yanda za su rika sanyawa a na mutunta Najeriya da ‘yan Najeriya.

AM Usman ya kara da cewa har yanzu akwai matsalar nan ta ‘yan mata da kan yi yunkurin fita ketare don aukawa karuwanci da aiyukan rashin mutunci; ya na mai cewa jami’an kan dakatar da matan da sanarwa hukumar hana fataucin mutane.

Konturolan ya ce su kan gano matan ta hanyar tambayar su inda za su je da kuma abun da za su yi, sai ka tarar VISA da ke nuna ziyara za a je amma sai matan su ce aiki za su tafi nema.

Hakanan AM Usman ya ce sam hukumar ba ta barin miyagun iri su tsallake bincike don irin na’urorin da hukumar ke amfani da su da kan fito da bayanan mutum da zarar ya danna tambarin hannun sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “KUSAN KULLUM SAI MUN SAMU ‘YAN NAJERIYA DA A KE DAWO DA SU DAGA KETARE – KONTUROLA”
  1. Your way of telling the whole thing in this
    piece of writing is actually pleasant, every one be capable of easily be
    aware of it, Thanks a lot.

Leave a Reply

Your email address will not be published.