• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KUNGIYAR TUNTUBAR JUNA TA AREWA TA SHAWARCI ‘YAN AREWA SU TAKAITA TAFIYA KUDU

Kungiyar tuntubar juna ta arewa ACF ta bukaci al’ummar arewa su dakatar da duk wata ziyara kudu musamman kudu maso gabar in ba ya zama dole ba.

ACF da nuna takaicin kisan gilla ga Ahmed Gulak a Imo, ta ce a na kashewa ‘yan arewa da ke zaune a kudu ko kai ziyara yankin kudu.

A sanarwa daga shugaban kungiyar Chief Audu Ogbeh, ACF ta yi gargadin masu tada fitinar su shiga taitayin su don hakan na daga dalilan yakin basasa a 1967.

kungiyar da ke kare muradun al’ummar yankin arewa mai jihohi 19

ACF ta ce burin masu kashe ‘yan arewa shi ne cimma burin su na kafa kasar Biafra; don haka shiga yankin su ya na da mstukae hatsari kuma in ba ya zama ala tilas sai an je ba to fasa tafiya ya fi ma’ana.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
14 thoughts on “KUNGIYAR TUNTUBAR JUNA TA AREWA TA SHAWARCI ‘YAN AREWA SU TAKAITA TAFIYA KUDU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.