• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KUNGIYAR TSARON NATO TA JANYE JAMI’AN TA DAGA KYIV BABBAN BIRNIN UKRAINE

A cigaba da zullumin yiwuwar mamaye Ukraine daga kasar Rasha, kungiyar tsaron yammacin turai NATO ta janye jami’an ta daga babban birnin kasar Kyiv.
NATO ta kai ma’aikatan birnin Lyiv da ke yammacin kasar Ukraine da Brussels babban birnin kasar Belgium.
Wasu kasashen turai sun janye jami’an diflomasiyyar su zuwa birnin Lyiv don ya na kan iyaka da Poland da hakan zai samar mu su kariya.
Shugaban NATO da helkwatar ta ke birnin Brussels Jens Stoltenberg ya ce Rasha na shirin gagarumin farmakin mamaye Ukraine.
Ukraine ba member NATO b ace don haka NATO ba ta dakaru a kasar sai dai ofishin tuntuba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “KUNGIYAR TSARON NATO TA JANYE JAMI’AN TA DAGA KYIV BABBAN BIRNIN UKRAINE”

Leave a Reply

Your email address will not be published.