• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KUNGIYAR TALLAFAWA SHUGABA BUHARI “PSC” TA DAKATAR DA AKPABIO

Kungiyar tallafawa shugaba Buhari a kamfen “PSC” ta dakatar da ministan Neja Delta Godwin Akpabio daga cikin ta don yanda ya yi biris da ‘yan kungiyar.

A gagarumin taro na kasa a Abuja, kumgiyar ta ce ta dakatar da Akpabio wanda shi ya jagoranci kungiyar gabanin zaben 2019 amma bayan lashe zabe sai su ka daina jin duriyar sa.
Kumgiyar wacce ta ambaci wasu ministoci da su ka zullewa kungiyar ciki har da karamar ministar Abuja, Ramatu Tijjani, sun ce matukar jami’an ba su gyara dabi’un yin nisa da dangi ba, to ba za su yi tafiyar zaben 2023 da su ba in Allah ya kai rai.

Daya daga na kan babbar tebur a kungiyar Injiniya Kailani Muhammed ya ce rashin kulawa da halin da sauran abokan gwagwarmaya ke ciki na nuna wadannan jami’an sun zama gafiya tsira da na bakin ki.
Hakanan shi ma dan kungiyar Danmalikin Kebbi, ya ce ya sha mamaki aiunun yanda ‘yan fadi tashin APC ke sanya kodaddun riguna tun da ita siyasa a duniya a ke cin gajiyar ta.

Za a iya cewa fitaccen wanda ya zo taron shi ne shugaban bankin lamunin gidaje Alhaji Ahmed Dangiwa da ke cewa shugaba Buhari ya ba wa marada kunya.
Har a ka tashi taron da ya samu halartar tsohon mai taimakawa shugaban kasa kan siyasa Gideon Sammani, a na jiran zuwan karamin ministan fetur Timipre Sylva bai zo ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3,023 thoughts on “KUNGIYAR TALLAFAWA SHUGABA BUHARI “PSC” TA DAKATAR DA AKPABIO”
 1. Howdy! I know this is kinda off topic however , I’d figured
  I’d ask. Would you be interested in exchanging links or maybe guest writing a blog post or
  vice-versa? My blog discusses a lot of the same topics as
  yours and I believe we could greatly benefit from each other.
  If you are interested feel free to shoot me an email. I look forward to
  hearing from you! Excellent blog by the way!