• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KUNGIYAR MA’ABOTA KAFAFEN LABARU TA KAFA KWAMITIN RIKO

Shahararriyar kungiyar nan ta masu sauraron rediyo wato “Kungiyar Ma’abota Kafafen Labaru” ta kafa kwamitin riko na kungiyar da zai yi aiki na tsawon shekara daya.

Kungiyar ta nada kwamitin karkashin jagorancin Buhari Yunusa Kumurya a wani taro a Abuja.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta dage wajen magance kalubalen tsaro musamman a arewacin Najeriya inda a kan samu ‘yan ta’adda su shiga kauyuka su hallaka mutane ba gaira ba dalili ko kuma miyagun iri su sace mutane su tsare su a daji don karbar makudan kudi.

Kazalika kungiyar ta bukaci samarwa matasa aiyukan yi da kawar da ‘yan yara kanana masu bara kan tituna.

Masu sharhi sun ce rashin kula da matasa ko kananan yara kan sa in sun girma su iya fadawa aiyukan ta’addanci ko fashi da makami.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.