Kungiyar larabawa ta gana da shugaban mulkin soja na Sudan Janar Abdelfattah Burhan kan juyin mulkin kasar.
Kungiyar na bukatar bangarorin da ke takaddama a kasar su tsaya kan tsarin maida mulki hannun farar hula cikin salama.
Kazalika tawagar kungiyar ta gana da firaministan kasar Mustapha Hamdok da sojojin su ka ture.
Kungiyar ta larabawa na son daukar gagarumin matakin sulhu a lamarin inda ta ke shirin tura babbar tawaga birnin Khartoum.
Sa bakin babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya sanya gwamnatin sojan amincewa da sako manyan ministocin farar hula da a ke tsare da su bayan juyin mulkin.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀