• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KUNGIYAR KWADAGON NAJERIYA TA JANYE YAJIN AIKI BAYAN SA’A BIYU DA FARAWA

Bayan taron da ya kai gwamnati da wakilan kwadago share tsawon lokaci har karfe biyu na safe a agogon Najeriya na litinin, kungiyar kwadagon ta amince da janye yajin aiki sa’a biyu bayan farawa don matsawa gwamnati lamba ta dawo da tallafin fetur ta kuma rage farashin wutar lantarki.

Gwamnatin Najeriya ta APC da ta sha sukar tsohuwar gwamnatin PDP kan karin farashin fetur gabanin lashe zabe a 2015, ta kara farashin litar fetur da kusan kashi 100% da ba a taba samun haka a tarihin gwamnatocin kasar tun samun ‘yanci a 1960. Wannan ya nuna karin farashin fetur ya zama al’adar gwamnatoci don lamuran kudin shiga da yanayin tattalin arzikin kasashe.
Bayanan janye yajin aikin sun nuna gwamnati za ta bullo da wasu shirye-shirye na tallafin rage radadi kamar yanda tsohuwar gwamnatin PDP ta yi; kazalika ta janye karin lantarki na tsawon mako biyu don nazarin matakin da ya fi dacewa.
Mataimakin sakataren hulda da kungiyoyi na kungiyar kwadagon Komred Nasir Kabir ya ce matakin yajin aikin duk da an janye ya samu nasara tun da akalla gwamnati ta dakatar da karin farashin lantarki.
Komred Kabir ya musanta cewa matsin lamba ya sanya kungiyar kwadagon janye yajin aikin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.