• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KUDURIN JERIN ZANGA-ZANGA A ABUJA KAN TABARBAREWAR TSARO DAGA DAIDAIKUN MUTANE

ByNoblen

Dec 12, 2021 ,

Tuni wasu ‘yan arewa akasari bisa jagorancin mata su ka kaddamar da wata zanga-zanga a Abuja don jan hankalin gwamnati ta dau matakan dakatar da kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yi musamman a arewa maso yamma.u
Duk da dai jami’an tsaro sun killace ‘yan zanga-zanga a iya dandalin “UNITY FOUNTAIN” wasu Karin mutane sun baiyana kudurin gudanar da karin zanga-zangar.
Ba mamaki tura tawaga da shugaba Buhari ya yi karkashin mai ba shi shawara kan tsaro Babagana Monguno zuwa arewa maso yamma amsa irin korafin kungiyoyi ne ciki da Jama’atu Nasril Islam da ke son matakai na zahiri.
Da alamun ‘yan zanga-zangar ba su yi la’akari da yanda ‘yan dawo-da-matan Chibok BBOG ba su kwashe nika da waka ba bayan tarwatsa su da a ka yi, sun yi alwashin tsayin daka sai sun bi ta titin nan na Shehu Shagari da ke daura da majalisar dokoki, kotun koli, fadar Aso Rock da helkwatar ‘yan sanda.
Daya daga jagororin zanga-zangar Zainab Ahmad ta yi tambayoyi ko mika bukatu ga gwamnati kan tsaron da ta ke ganin in haka ta tadda ruwa za a samu sararawa.
A daidai lokacin da a ke wannan batu na tsaro, wata kungiyar cigaban Funtua karkashin limamin masallacin ZONE B na gidajen ‘yan majalisar taraiya Ibrahim Auwal Usama, ta ce za ta shigar da shugaba Buhari kara matukar ba a janye shirin karin farashin fetur ba zuwa nan da mako uku.
Haka rayuwa ta ke wasu na kuka wasu na dariya a kasashen da akasarin mutane ba su tsallake mizanin talauci na majalisar dinkin duniya na samun dala daya a wuni ba, wato yanzu wajen Naira 560 a kasuwar canji.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “KUDURIN JERIN ZANGA-ZANGA A ABUJA KAN TABARBAREWAR TSARO DAGA DAIDAIKUN MUTANE”

Leave a Reply

Your email address will not be published.