• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KUDI DA YAWAN GWAMNONI NE APC TA FI MU-BUBA GALADIMA

Jigon jam’iyyar adawa ta NNPP Injiniya Buba Galadima ya ce APC mai mulki da dan takarar ta Bola Tinubu ta fi su yawan gwamnoni da kudi ne.

Galadima wanda ya ke magana kan ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun da ke kan gaba, ya yi hasashen Kwankwaso ka iya lashe zaben a kada kuri’a zagayen farko amma ba mamaki zaben ya iya kai wa zagaye na biyu.

Buba Galadima ya bugi kirjin NNPP za ta lashe zaben jihar Kano da Lagos da sauran sassa masu yawan kuria.

Duk da haka Galadima ya nuna tababar yiwuwar lashe zaben NNPP a jihar sa ta Yobe da Borno.

Manyan ‘yan takara dai a zaben shugaban Najeriya na 2023 mai zuwa sun hada da Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi.

Hakanan akwai wasu ‘yan takarar da manyan mutane ne ko da jam’iyyun su bas u yi fice ba kamar Manjo Hamza Almustapha.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.