• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KU TABBATAR KUN BI KA’IDAR ZABE A WAJEN GUDANAR DA AIKIN KU – INJI SHUGABAN HUKUMAR ZABE MAHMUD YAKUBU GA MA’AIKATAN SA

ByYusuf Yau

Sep 19, 2020 , ,

Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu ya gargadi jami’an hukumar ta sa, da za su gudanar da zaben gwamnan Edo su bi ka’idar aikin. Yakubu wanda ya karantawa jami’an ka’idar aikin zabe, ya hore su kar su yarda su fifita wata jam’iyya kan wata a lokacin gudanar da zaben. Hakanan shugaban hukumar ya ce har kullum jami’an su tabbatar da bin ka’ida don idon duniya na kan Najeriya a kan lamuran zabe. In za a tuna Amurka ta aza takunkumin hana ba da damar shiga kasar ta ga wasu ‘yan siyasar Najeriya da ta ce sun ba da gudunmawa wajen rashin adalci a zaben gwamnan Kogi da na jihar Bayelsa. Amurka ta bukaci jami’an siyasar Najeriya su tabbatar da adalci a zaben jihar Edo.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “KU TABBATAR KUN BI KA’IDAR ZABE A WAJEN GUDANAR DA AIKIN KU – INJI SHUGABAN HUKUMAR ZABE MAHMUD YAKUBU GA MA’AIKATAN SA”
 1. Hi there! I realize this is sort of off-topic however I needed to ask.
  Does running a well-established blog like yours require a lot of work?
  I am completely new to running a blog but I do write in my journal on a daily
  basis. I’d like to start a blog so I can share my experience and feelings online.
  Please let me know if you have any recommendations or tips for brand new aspiring blog
  owners. Thankyou!

 2. Oh my goodness! Amazing article dude! Many thanks,
  However I am going through issues with your RSS.
  I don’t understand the reason why I cannot join it.
  Is there anyone else having similar RSS problems?
  Anyone who knows the solution can you kindly respond?
  Thanx!!

Leave a Reply

Your email address will not be published.