Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ja hankalin ‘yan jam’iyyar sa ta APC da gujewa duk abun da zai iya kawo cikas a babban taron jam’iyyar na zaben sabbin shugabanni a asabar din nan.
Shugaban wanda ya gana da shugabannin kungiyar ‘yan jam’iyyar na majalisar dokoki wadanda su ka kai ma sa ziyara, ya bukaci ‘yan jam’iyyar su hada kai ta hanyar tinkarar duk wani zabe nan gaba da karsashin samun nasara.
Tun gabanin nan shugaban ya gana da gwamnonin jam’iyyar da kuma ‘yan takarar neman shugabancin jam’iyyar.
An tsegunta cewa shugaban na mara baya ga tsohon gwamnan Nassarawa Abdullahi Adamu don zama sabon shugaban jam’iyyar.
Babban zaben da ke tafe a febrerun badi zai zama mai kalubale ga jam’iyyar don shugaba Buhari ba zai tsaya takara ba a lokacin don karewar wa’adi.
KU GUJEWA ABUN DA ZAI KAWAR MANA NASARA – SHUGABA BUHARI

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀