• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTUNAN NAJERIYA NA CIGABA DA YAJIN AIKI

Kotunan Najeriya sun shiga yajin aiki inda hakan ya dakatar da zaman sauraron shari’u a dukkan matakai.

Kungiyar ma’aikatan kotuna ta jagoranci ma’aikatan su auka wannan yajin aikin don samun damar cin gashin kan lamuran kudi na kotuna.

An ruwaito babban alkalin Najeriya Muhammad Tanko na cewa janye yajin aikin ya fi alheri don ba da damar duba korafin ma’aikatan na shari’a.

Tanko ya ce ba ya son tuntubar jihohi don sa baki a lamarin don hakan zai zama tamkar neman alfarma da su kuma daga bisani za su nemi fanshewa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *