Babbar kotun Lagos ta yanke hukuncin kisa kan dan kasar Denmark mai suna Peter Nielson wanda a ka samu da laifin kashe matar sa da ‘yar sa ‘yan Najeriya.
Nielson ya kashe matar ce mai suna Zainab a gidan su da ke anguwar tsibirin Banana.
An gurfanar da Nielson a gaban kotu tun shekara ta 2018 inda a ka caje shi da aikata laifukan kisan gilla guda biyu.
Alkalin kotun Bolance Okikiolu-Ighile ya yanke hukuncin a kashe Nielson ta hanyar rataya.
Mutumin ya ki amsa laifukan da a ka tuhumar sa amma kotu ta yanke hukuncin a aika shi lahira.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
hello!,I like your writing so much! share we communicate more about your article on AOL? I need an expert on this area to solve my problem. May be that’s you! Looking forward to see you.
Regards for helping out, superb info .