• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTUN MAJISTARE A ABUJA TA TURA SOWORE ADANA KAFIN DUBA BUKATAR BELI

Kotun majistare a Abuja ta tura Omoyele Sowore ma’adana a Kuje gabanin duba bukatar ba da belin sa.

Sowore wanda shi ne mawallafin jardar yanar gizo ta sahara kazalika ya jagoranci zanga-zangar juyin juya hali da ‘yan sanda su ka zarge shi da yunkurin kifar da gwamnati ko cin amanar kasa.

Wannan karo ‘yan sanda sun kama Sowore da gurfanar da shi gaban kotu don zargin sa da tada fitina.

Sowore ya ce ya shiga kare masu zanga-zangar endsars ne inda ya ce ‘yan sanda sun yi dirar mikiya a kan sa har da fasa ma sa hanci.

Alkalin kotun Mabel Segun Bello ya tsayar da talatar nan don duba neman belin Sowore.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “KOTUN MAJISTARE A ABUJA TA TURA SOWORE ADANA KAFIN DUBA BUKATAR BELI”
  1. I don’t even know how I ended up here, but I thought this post was great.
    I do not know who you are but definitely you’re going to a famous blogger if you are not
    already 😉 Cheers!

  2. Thanks for sharing your info. I truly appreciate your efforts and I
    will be waiting for your further write ups thanks once again.

Leave a Reply

Your email address will not be published.