Kotun ma’aikata ta Najeriya ta ba da umurnin dakatar da kungiyar kwadago NLC daga fara shiga zanga-zanga da yajin aiki ranar litinin mai zuwa 28 ga watan nan na satumba.
Alkalin kotun Ibrahim Galadima ya kira kungiyar kwadagon ta zo kotu ranar 12 ga watan gobe don sauraron karar da wata kungiyar farar hula ta shigar don kalubalantar shiga yajin aikin kan kara kudin litar fetur da wutar lantarki.
Alkalin ya bukaci jami’an tsaro su kare ma’aikatan da in sun zabi yin biris da umurnin kungiyar kwadagon su zo aiki.
A baya dai kungiyar kwadago ba ta sauraron umurnin kotun kafin aukawa yajin aikin duk da ba lalle ne kwalliya ta biya kudin sabulu ba.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀