• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTUN KOLIN NAJERIYA TA MUSANTA SAHIHANCIN JERIN SUNAYEN ZAMA BABBAN LAUYA NA BANA

ByYusuf Yau

Aug 19, 2021 , , , ,

Kotun kolin Najeriya ta musanta jerin sunaye da ke yawo a yanar gizo da ke nuna na lauyoyi ne da za a yi wa karin daraja zuwa matsayin manyan lauyoyi wato SANS.

Kakakin babbar kotun Festus Akande ya ce sam jerin sunayen a yanar gizo ba shi da sahihanci ko kadan.

Akande ya zargi masu yada jerin sunayen da neman haddasa rudani kan aikin kwamitin zabar lauyoyin da za a daga darajar ta su.

Akande ya ce da zarar an kammala fitar da sunayen daga lauyoyin da su ke reman darajar za a wallafa a fitattun jaridu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *