• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTUN KOLIN NAJERIYA TA BA WA HUKUMAR ZABE HURUMIN SOKE JAM’IYYUN SIYASA

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hurumin da hukumar zabe ke da shi na soke jam’iyyar siyasa da ba ta cika sharudda ba ko ta saba ka’aida.

Babbar kotun da a ke yi wa kirari da kotun Allah ya isa, ta yanke hukunci ne da ya tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na soke wata jam’iyyar siyasa.

Lamarin ya faru ne bisa daukaka kara da daya daga jam’iyyun siyasar da a ka soke NUP ta yi na kalubalantar hurumin hukumar zabe na soke ta.

Kotun kolin ta ce hukumar zabe ta yi amfani da hurumin ta na tsarin mulki ne ya sa ta soke jam’iyyar.

Duk da haka akwai sauran karar wasu jam’iyyu 22 a gaban kotun kolin da su ke son a haramta soke su da hukumar zaben ta yi.

Jam’iyyun 22 sun samu nasara a hukuncin kotun daukaka kara kan hukumar zaben.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.