• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTU ZA TA YANKE HUKUNCI KAN BARAWON MUTANEN NAN EVANS A WATAN FEBRERUN BADI

ByNoblen

Dec 11, 2021 ,

Kotu a Ikeja Lagos za ta yanke hukunci kan gagarumin barawon mutanen nan Evans ranar 25 ga watan Febrerun badi.
In za a tuna tsohon jami’in aiki da cikawa na ‘yan sanda Abba Kyari ya cafke Evans da gurfanar da shi gaban kotu.
A na tuhumar Evans da sauran abokan satar sa da su ka hada da
Okwuchukwu Nwachukwu, Ogechi Uchechukwu, Chilaka Ifeanyi, Victor Aduba da Uche Amadi.
Lauyan Evans mai suna Victor Opara bukaci babbar kotun ta jihar Lagos ta sake Evans, ya na mai cewa wai ba a same shi da laifin da a ke zargin sa da shi kai tsaye ba.
Bai zama abun mamaki ba yanda sauran wadanda a ke tuhuma su ka cewa kotun ba su aikata tuhumar biyu da a ke yi mu su ba.
Tuhumar ta hada da sace mutane da hada baki wajen sace mutane don karbar kudin fansa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *