• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTU ZA TA FARA SAURARON KALUBALANTAR SAUYA SHEKAR MATAWALLE ZUWA APC

Babbar kotun taraiya a Abuja za ta fara sauraron karar kalubalantar gwamnan Zamfara Bello Matawalle don sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Wasu ‘yan PDP daga Zamfara su biyu su ka shigar da karar da nuna Matawalle ba shi da hurumin sauya sheka bisa hukuncin kotun koli da ya ba shi dama ya zama gwamna bayan ture nasarar APC da gwamna mai jiran gado Shehu Mukhtar Kogunan Gusau.

Babbar jam’iyyar adawa PDP ta bukaci a shigar da ita cikin masu shigar da karar.
Mataimakin gwamnan Mahdi Aliyu Gusau bai bi gwamnan wajen sauya sheka ba.
Za a fara sauraron karar ranar 16 ga watan nan da kuma a ke ganin karar ka iya tafiya har kotun koli.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *