• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTU TA TURA SANATA NDUME GIDAN WAKAFI DON RASHIN ABDULRASHID MAINA KOTU

Alkalin babbar kotun Abuja Jostis Okon Abang ya ba da umurnin tura Sanata Ali Ndume gidan wakafi don rashin halartar Abdulrashid Maina kotu da Ndumen ya tsayawa har a ka ba da belin sa.

EFCC ce ta shigar da tsohon shugaban kwamitin aiki da cikawa kan fansho Abdulrashid Maina gaban kotu da caji 12 na zargin badakalar Naira biliyan 2.

Ali Ndume ya tsayawa Maina a ka ba da belin sa kan Naira miliyan 500 amma rashin zuwan sa kotu ya sa alkalin Abang soke belin.

Yanzu dai an tura Ndume gidan yarin Kuje da kuma umurtar sa ya fadi me ya sa gwamnati ba za ta amshe Naira miliyan 500 da a ka zuba wajen samun belin ba.

Ndume ya ce a matsayin na dan majalisar dattawa mai wakiltar Maina, ya amince ya karbi belin bayan matar Maina,Kawu da mahaifiyar sa sun tunkare shi don batun belin.

Hakanan Ndume ya ce ya dauka ya tsayawa Maina ne don ya rika halartar kotu a duk lokacin da ta ke zama kan karar

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “KOTU TA TURA SANATA NDUME GIDAN WAKAFI DON RASHIN ABDULRASHID MAINA KOTU”
 1. I got this website from my friend who informed me
  concerning this web site and at the moment this time I am visiting this website
  and reading very informative posts here.

 2. After I originally left a comment I seem to have clicked on the -Notify me when new
  comments are added- checkbox and from now on each time a comment
  is added I get four emails with the exact same comment.
  There has to be an easy method you can remove me from that service?
  Thanks!

 3. Excellent way of telling, and fastidious paragraph
  to get information about my presentation focus, which i am going to convey in academy.

Leave a Reply

Your email address will not be published.