• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTU TA SANAR DA RANAR SAURARON KARA KAN DUKIYAR PATIENCE JONATHAN

Babbar kotun taraiyar Najeriya a Lagos ta sanar da cewa ranar 7 ga watan oktoba za ta saurari kara kan ma’ajiyar kudin wasu kamfanoni da a ka alakanta mallakar su ga uwargidan tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

Kudin dai sun hada da dala miliyan 5.78 da Naira biliyan 2.4.

Hukumar yaki da cin hanci EFCC ta shigar da karar bukatar karbe kudin da dawo da su asusun gwamnati.

Alkalin kotun T.G. Ringim ya ba wa humumar ta EFCC damar yin bayanai don ba da hujjar bukatar karbe kudin.

Tun 2017 kotu ta ba da umurnin a rike kudin har sai an kammala sauraron shari’ar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *