• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTU TA SAKI EL-ZAKZAKY DA MATAR SA

Wata babbar kotun jihar Kaduna karkashin jagorancin Alkali Gideon Kurada, ta saki shugaban kungiyar ‘yan shi’a a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky da matar sa Zinatu.

A hukuncin da ya kwashe sama da awanni takwas, a ranar Laraba, alkalin, Gideon Kurada, ya goyi bayan gabatar da karar da Ibrahim El-Zakzaky da matarsa ​​suka gabatar.

Masu sharhi na ganin sako Ibrahim Elzakzaky da babbar kotun Kaduna ta yi zai rage maida hankali da ‘yan shia su ka yi kan Abduljabbar Kabara da su ke marawa baya sabanin matsayin manyan malaman Kano.

Yayin da Abduljabbar ke hannun jami’an tsaro don jiran shari’a a Kano, ‘yan shia na El-zakzaky sun fito wasu garuruwan arewacin Najeriya su na buga gangunan murnar sako shugaban su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2,361 thoughts on “KOTU TA SAKI EL-ZAKZAKY DA MATAR SA”