• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTU TA KORI KARAR GWAMNONI DA KE NEMAN GWAMNATIN TARAIYA TA RIKA DAUKAR NAUYIN KOTUNAN JIHOHI

Kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin korar karar da gwamnono su ka shigar sun a bukatar a mika alhakin daukar nauyin kotunan jihohin kan gwamnatin taraiya.
Kwamishinonin shari’a na jihohi 36 su ka shigar da karar sun a bukatar a daura alhakin samar da kudin aikin manyan kotunan jihohi, kotun daukaka kara ta musulunci da ta al’adun gargajiya.
A hukuncin da alkalai 4 su ka rinjayi 3, kotun kolin ta ki amincewa da bukatar jihohin don haka za su cigaba da daukar dawainiyar kotrunan su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.