• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KOTU TA DAKATAR DA ZABEN SHUGABANNIN APC A TARABA HAR SAI TA KAMMALA SAURARON RASHIN AMINCEWA DA ZABEN

ByNasiru Adamu El-hikaya

Oct 25, 2021

Babbar kotun taraiya a Jalingo jihar Taraba, ta dakatar da zaben shugabannin jam’iyyar APC a jihar Taraba har sai an kammala sauraron karar kalubalantar zaben.
Rahoto ya nuna wasu sashen ‘yan jam’iyyar sun aiyana tsohon shugaban jam’iyyar Elsudi Ibrahim Tukur a matsayin wanda su ka amince ya zarce da shugabanci.
Nan take sashen ‘yan jam’iyyar su ka ruga kotu inda su ka bukaci ta yi watsi da duk batun wani zabe don a bi ka’idojin yin zabe bisa dokokin jam’iyya.
Daya daga masu karar Alhaji Abdullahi Ade ya ce sun mika bukata ga kotu don samun adalci.
A talatar nan za a fara sauraron karar.
Sauran masu kalubalantar zaben sun hada da Alhaji Mohammad Sani Tullu, Ajuju Muktar, Sambo Tukur Alhaji da Barista Bilyaminu Lukman Maihanchi.
An samu rigima a zaben APC na jihohi inda a wasu jihohin kamar Kano da Bauchi a ka gudanar taruka biyu da fitar da shugabanni biyu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “KOTU TA DAKATAR DA ZABEN SHUGABANNIN APC A TARABA HAR SAI TA KAMMALA SAURARON RASHIN AMINCEWA DA ZABEN”
  1. When I initially commented I clicked the “Notify me when new comments are added” checkbox and
    now each time a comment is added I get three e-mails with the same
    comment. Is there any way you can remove me from
    that service? Thank you!

Leave a Reply

Your email address will not be published.