• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KORONA-SAUDIYYA ZA TA DAGE DOKAR HANA WASU KASASHE SHIGA KASAR TA

ByYusuf Yau

Nov 26, 2021

Saudiyya ta baiyana cewa za ta janye dokar hana ‘yan kasashe 6 da ta hana shigowa don yaki da annobar korona bairos.
Ma’aikatar cikin gida ta Saudiyya ta ba da sanarwar janye hana mutan kasashen shigowa don alamun sauke da a ke samu kan cutar.
Kasashen dai sun hada da Indunusiya, Pakistan, Brazil, Vietnam, Masar da Indiya.
Saudiyya ta ce duk wanda ya samu cikekken rigakafin korona daga kasashen zai iya shigowa ba tare da umurnin yawo a wasu kasashe na tsawon kwana 14 ba kafin samun damar shigowa.
Duk da haka in mutane daga kasashen sun shigo za su kebe kan su na kwana biyar don tabbatar da koshin lafiyar su.
Sabon tsarin zai fara aiki daga daya ga watan gobe.
Duk wadannan alamu ne na yiwuwar gudanar da aikin hajjin bana da alhazai daga kasashen ketare.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.