• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KORONA: Pfizer YA SAMAR DA MAGANIN KORONA

Shaharerren kamfanin maganin nan na duniya Pfizer ya ce maganin da a ke hadawa na magance cutar korona ya nuna tasirin aiki kashi 90%.

Wannan wata nasara ce da ta zo bayan alkaluman wadanda su ka mutu sanadiyyar cutar a duniya ya kai mutum miliyan 1.2.

A Amurka kadai kusan mutum dubu 250 su ka mutu sanadiyyar kamuwa da cutar ta mashako.

Jami’in kamfanin Pfizer mallakar Amurkawa  Dr. Bill Gruber ya ce sun samu kwarin guiwar hada wannan magani.

Kamfanonin magani na duniya na ta aikin hada magani da zai magance wannan cuta da ta kawo koma baya a lamuran duniya.

Shugaba Donald Trump ya ce hada wannan magani babban labari ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.