• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

KORONA-MA’AIKATAN NAJERIYA NA BAIYANA RA’AYOYI MABAMBANTA KAN UMURNIN LALLE SAI SUN YI RIGAKAFI

ByHassan Goma

Oct 19, 2021
Ma’aikatan gwamnatin taraiyar Najeriya na baiyana ra’yoyi mabambanta kan umurnin lalle sai sun yi rigakafin korona bairos.
Hakan na zuwa ne gabanin fara aikin dokar hana shiga ma’aikata ga duk wanda ya gaza yin rigakafin zuwa daya ga watan disamba, matukar bai nuna shaidar gwajin lafiya ba.
Ma’aikatan dai sun rabu ne tsakanin wadanda wa imam sun yi rigakafin, ko kuma masu niyyar yi da kuma wadanda ke daukar hakan wata hanya ce ta gallazawa kan rigakafin da su ke tababar sahihancin sa ga lafiyar su.
Dr.Mukhtar Muhammad na kwamitin yaki da korona na shugaban kasa ya ce ba daga kafa ga wanda ya bijirewa umurnin.
Ponfa Audu da ke aiki a birnin taraiya Abuja ya ce tsaida ranar daya ga disamba bai dace ba don hakan zai jefa ma’aikata da yawa masu kin jinin allurar cikin zullumi da zai hana su sakat a bakin aiki.
Audu ya kara da baiyana akwai ma jita-jitar da ke nuna wasu dillalai za su iya samarwa wasu shaidar rigakafin ta bogi.
Shi kuma darakta a gwamnatin taraiya Baba Sani ya shawarci ma’aikata su yi wa kan su kiyamul laili wajen karbar rigakafin.
Daraktan tsare-tsare da bincike na hukumar lafiya matakin farko Dr.Abdullahi Bulama ya ba da tabbacin akwai wadatar alluran rigakafin ga dukkan ma’aikatan.
In ka debe ma’aikata da a ka tilasta mu su yin rigakafin, akwai ‘yan kasa marar sa adadi da sam ba su yarda da rigakafin ba.
Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “KORONA-MA’AIKATAN NAJERIYA NA BAIYANA RA’AYOYI MABAMBANTA KAN UMURNIN LALLE SAI SUN YI RIGAKAFI”
 1. Hi there, I discovered your blog via Google
  whilst looking for a related subject, your site got here up, it appears great.
  I’ve bookmarked it in my google bookmarks.
  Hello there, simply become aware of your blog thru Google, and located that it is really
  informative. I’m going to watch out for brussels. I’ll appreciate for
  those who continue this in future. Many folks might be benefited from
  your writing. Cheers!

Leave a Reply

Your email address will not be published.